Isa ga babban shafi
Colombia

Colombia ta sake kulla yarjejeniya da ‘Yan tawaye

Gwamnatin Colombia da ‘Yan Tawayen kungiyar FARC sun sanar da shirin sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya domin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 52 ana yi a kasar.

An shafe lokaci gwamnatin Colombia na tattaunawa da 'yan tawayen FARC
An shafe lokaci gwamnatin Colombia na tattaunawa da 'yan tawayen FARC REUTERS/Enrique de la Osa
Talla

Bangarorin biyu sun ce, za a mikawa Majalisa sabuwar yarjejeniyar da aka yi wa sauyi daga wadda ‘yan kasar suka ki amincewa da ita domin samun goyan baya.

Shugaban kasa Juan Manuel Santos ya ce sabuwar yarjejeniyar ta kawar da wasu daga cikin fargabar da ‘yan adawa ke yi, cikin su har da tsohon shugaban kasa Alvaro Uribe.

Sai dai tsohon shugaban kasar Alvaro Uribe ya ce bai dace a ba ‘Yan Tawayen damar shiga siyasa a dama da su ba, saboda irin ta’addancin da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.