Isa ga babban shafi
Al Qaeda

Shugabannin Al Qaeda da IS na cacar baki akan Shi’a

Shugaban kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri ya caccaki Abu Bakr al-Baghdadi shugaban mayakan IS masu da’awar jihadi a Syria da Iraqi a wani sakon murya da ya fitar a ranar Alhamis.

Abu Bakr Baghdadi shugaban kungiyar IS da Ayman Zawahiri shugaban kungiyar Al Qaeda
Abu Bakr Baghdadi shugaban kungiyar IS da Ayman Zawahiri shugaban kungiyar Al Qaeda REUTERS
Talla

Zawahiri ya kira Baghadadi a matsayin makaryaci  da ke yada farfagandar karya.

Zawahiri ya mayar da martani ne ga Baghadadi bayan ya ce Al Qaeda na adawa da hare haren da ake kai wa ‘Yan Shi’a sannan kungiyar na kawance da shugabannin Kiristoci.

Shugaban na Al Qaeda ya karyata zargin na Baghdadi akan rashin kyamar Shi’a, inda ya ce ya yi kira ne a dai na kashe fararen hula da sunan kai wa ‘Yan Shi’a hari.

Sannan Zawahiri ya karyata batun ya ce Kiristoci na iya zama abokan tafiya ga gwamnatin daular musulunci da suke fatar kafawa.

Ya ce abin da ya ke nufi shi ne Kiristoci na iya tafiyar da harakokinsu karkashin tsarin gwamnatin daular Islama.

Al Qaeda da IS da ke kiran kansu Sunni sun kashe mabiya Shi'a da dama da mabiya addinin Kirista.

Amurka da manyan kasashen duniya na neman shugabannin kungiyoyin biyu na ‘Yan ta’adda ruwa a jallo wadanda suka jagoranci daruruwan hare hare akan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.