Isa ga babban shafi
Syria

Assad ya shirya ganawa da 'yan tawayen Syria

Shugaban Syria Bashar al- Assad ya ce, a shirye yake ya zauna kan teburin sulhu da kungiyoyi 100 na ‘yan tawayen kasar da ke yaki da gwamnatinsa, matukar sun amince su ajiye makamansu.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad SANA/Handout via REUTERS
Talla

A cikin wannan watan ne, gwamnatin Syria da ‘yan tawayen kasar za su gana a birnin Astana na Kazakhstan don kawo karshen ricikin shekaru shida da ya lakume rayuka fiye da dubu 300 a karkashin jagorancin kasashen Rasha da Turkiya.

Wani dan siyasar Faransa da ke ziyara a Syria, Thierry Mariani ya ce, sai dai shugaba Assad ba zai cimma wata yarjejeniyar sulhu da mayakan jihadi ba.

Gwamnatin Syria ta kuma yi watsi da zargin da ake yi wa dakarunta na aikata laifukan yaki kan fararen hula a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.