Obama zai gabatar da jawabin bankwana a Chicago
A wannan talata Barack Obama zai gabatar da jawabin bankwana a matsayinsa na shugaban Amurka bayan share tsawon shekaru 8 a kan karagar mulki.
Wallafawa ranar:
A lokacin gabatar da wannan jawabi, Obama ya zabi birnin Chicago ne domin gabatar da wannan jawabi tare da matarsa Michelle da kuma mataimakinsa Joe Biden.
A cikin kwanaki 10 masu zuwa ne Obama zai mika ragamar mulki a hannun sabon shugaba Donald Trump.
Mista Trump mai jiran gado ya lashi takobin kawar da martabar Obama a Amurka bayan kaddamar da suka ta hannu hagu da dama.
Zaben shekarar 2016 a Amurka ya diga ayar tambaya kan sahihancin tsarin demokrudiya a kasar.
Jawaban Obama mai barin Mulki a yau zai mayar da hankali ne wajen karfafa gwiwar wadanda ke bayyana furgabansu da jagoranci Trump.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu