Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na sa-in-sa da Jami’an asirin Amurka

A yayin da ya rage mako guda ya karbi ragamar shugabancin Amurka, Donald Trump ya fara sa-in-sa da jami’an leken asirin Amurka wadanda ya zarga da haddasa fallasar wani mummunan rahoton rayuwar shi da karuwai da alakar shi da Rasha wanda ya karyata.

Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump.
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump. REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Donald Trump ya zargi hukumomin leken asirin da kokarin yi ma shi zagon kasa.

Rahoton na kunshe da wasu bayanai da bidiyo marar dadi akan Trump, wadanda ya bayyana cin mutunci tare da kwatanta fallasar tamkar ta gwamnatin Nazi.

Daraktan hukumar leken asirin Amurka James Clapper ya kira shugaban mai jiran gado ta wayar tarho inda ya ke shaida masa cewa babu hannunsu a fallasar.

Wani tsohon Jami’in hukumar leken asirin M16 ta Birtaniya ne ya gudanar da binciken akan Trump da ke kunshe da rayuwar shi da karuwai a Rasha.

Kafar BuzzFeed ce kuma da ke yada labarai a Intanet a Amurka ta fara wallafa labarin cewa binciken MI6 na cikin batutuwan da manyan Jami’an FBI da CIA da NSA suka gabatar wa Trump.

Trump ya daura laifin akan hukumomin na Amurka da ya ce bai kamata su bari irin wannan labarin na karya ya kai ga hannun jama'a ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.