Isa ga babban shafi
US

Babbar Kotun Amurka ta hana aiwatar da matakin koran baki

Wata Babbar Kotun Amurka ta dakatar da sabuwar doka da Shugaba Donald Trump ya zartas juma'a don hana baki ‘yan kasashen waje musamman musulmi shiga kasar Amurka.

Wasu masu bore a filin jiragen sama na JFK dake New York dake adawa da matakin Donald Trump
Wasu masu bore a filin jiragen sama na JFK dake New York dake adawa da matakin Donald Trump REUTERS/Stephen Yang
Talla

Hukuncin Kotun na bukatar a dakatar da hana ‘yan gudun hijira da sauran bakin haure  da suka makale a filayen jiragen sama dake neman shiga Amurkan.

Matakin Kotun na zuwa ne a wani lokaci da aka sami dimbin baki ‘yan kasashen waje da suka makale a tashoshin jiragen sama dake fara bore saboda hana su izinin shiga kasar.

Kungiyar American Civil Liberties Union wadda lauyanta ya maka Amurkan gaban kotu saboda daukan matakin  sun yi ta nuna farin ciki da hukuncin kotun.

Shekaranjiya Juma'a Shugaba Donald Trump ya sanya hannu cikin wannan doka dake hana baki ‘yan gudun hijira shiga Amurka na tsawon kwanaki 120, sannan kuma aka hana musulmi daga kasashe 7 tsoma kafarsu cikin Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa tsauraran matakan hana musulmi bakin haure shiga Amurka da ya fara aiwatarwa na aiki sosai.

A daya gefen kuma,Shuwagabannin kamfanonin  kera konfutoci ne, suka bayyana adawarsu da matakin na shugaba Trump

 kamfanin Twitter, da mafiyawan amerikawa ke amfani da shi  wajen aika sakonni ya  bayyana goyoyan bayansa ga bakin.

Shugabanin  kamfanonin , Facebook, Netflix, Google da Microsoft sun hada kai wajen nuna rashin amincewa, da zulakanta baki musaman musulmi a kasar ta Amruka,  inda suka ce daga yanzu za su baiwa injiniyoyin kofuta da suka fito daga  kasashen larabawan da hanin ya shafa a guraben ayukan yi  a kamfanoninsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.