Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na gab da hana baki shiga Amurka

A wannan larabar ake saran shugaban Amurka Donald Trump zai sanya hannu kan dokokin takaita shigar baki kasar kamar yadda ya bayyana lokacin yakin neman zabensa.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin da ya sanya hannu janye Amurka daga shirin kasuwancin TPP
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin da ya sanya hannu janye Amurka daga shirin kasuwancin TPP SAUL LOEB / AFP
Talla

Rahotanni sun ce dokokin za su takaita bai wa bakin da suka fito daga kasashen Iraqi da Iran da Libya da Somalia izinin shiga Amurka.

Sauran kasashen da dokar zata shafa sun hada da Sudan da Syria da Yemen

A sakon da Trump ya aika ta kafar twitter ya ce lallai za su gina katangar da ya yi alkawari tsakanin Amurka da Mexico.

Kasa da mako guda da kama aiki, Mista Trump, ya aiwatar da muradai da dama sune jigo a yakin neman zaben da ya  kayar da Hillary Clinton.

Shugaba Trump ya ce aikinsa shi ne kare Amurka da muradunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.