Tayar da komadar Nono na sanadin ajalin mata a Amurka
Hukumomin Lafiya a kasar Amurka sun ce mata 9 ne yanzu haka aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon cutar kansa biyo bayan aikin tada komadar nonon su da aka yi.
Wallafawa ranar:
Hukumomin sun ce sun samu rahotanni 359 daga matan da aka yi wa irin wannan aiki na tada komadar nono da ke fama da cutar kansa kuma 9 daga cikinsu sun sheka lahira.
Rahotan ya ce Amurka ta amince da rahotan Hukumar Lafiya ta Majalisar dinkin Duniya cewar sinadarin Anaplastic Large-Cell Lymphoma da ake amfani da shi wajen yi wa matan aiki na yi musu illa.
Shekaru biyu da suka gabata Cibiyar yaki da cutar kansa a Faransa ta yi gargadi kan nasabar tiyatar Nono da cutar kansa.
Kansar Nono na cikin manyan cututukan da ke ajalin Mata a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu