Argentina ta kama wani mutun da Faransa ke nema ruwa ajallo
Wani tsohon jami'in tsaro na kasar Argentina da ake zargi da salwantar da rayukan mutane da yawa tsakanin shekara ta 1970 zuwa 1980, amma ya bace, ya shiga hannun jami'an tsaro a Bounos Aires inda aka kama shi da ransa.
Wallafawa ranar:
Tsohon Kanar Jose Osvaldo ‘Balita’ Ribeiro ya kasance mutun na biyu a Bataliya ta 601, bangaren sojan da ake zargi da salwantar da rayukan daruruwan mutane ‘yan adawa a wancan lokaci.
A bayan idanunsa aka zartas masa da hukuncin dauri na shekaru 35 a Faransa cikin shekara ta 2010 saboda bacewar wasu mutane biyu ‘yan kasar Faransa da Chile , kuma tun lokacin Faransa ke godon Argentina ta kamo shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu