Isa ga babban shafi
Argentina

Tsohon Shugaban Argentina Zai Tsaya Takaran Majalisa don kaucewa kamashi

Wani tsohon Shugaban kasar Argentina Carlos Menem mai shekaru 86 a duniya ya sake bayyana niyyarsa na tsayawa zabe a kasar ta su, wannan karon a matsayin dan majalisa, a wani matakli da ake ganin dabara ce domin ya tsallake dukkan matakin kamashi da ake shirin yi saboda wasu laifuka da ya aikata.

Shugaba Mauricio Macri na kasar Argentina
Shugaba Mauricio Macri na kasar Argentina REUTERS/Agustin Marcarian
Talla

Carlos Menem ya shugabancin kasar ta su tsakanin shekara ta 1989 zuwa 1999 kuma daga baya yayi sanata har aka sameshi da laifin safarar makamai da cin hanci da rashawa, to amma saboda rigar kariya don yana wakilin majalisa ba’a kama shi ba don gurfanar dashi gaban kotu.

Idan har ya yi nasara ya sake tsayawa takaran shugabancin kasar zai kasance shekarunsa 91 a lokacin da zai kammala wa’adin shekaru hudu na farko a zaman majalisar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.