Isa ga babban shafi
korea ta Arewa-MDD

MDD ta kakaba sabbin takunkumai kan Korea Ta Arewa

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin Amurka na tsananta takunkumai kan Korea Ta Arewa bisa gwaje-gwajenta na makami mai linzami.

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un
Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un KCNA/Handout via REUTERS/File Photo
Talla

Daga cikin sabbin takunkuman da Kwamitin ya amince da su a wannan Asabar, akwai batun haramta wa Korea Ta Arewa fitar da kayyakinta zuwa kasashen ketare, abin da zai janyo ma ta asarar Dala biliyan 1 a kowacce shekara.

A karon farko kenan da Kwamitin Sulhun ya dauki irin wannan matakin kan kasar tun bayan darewar shugaba Donald Trump kan karagar mulkin Amurka.

Kazalika, akwai yiwuwar China ta dauki na ta matakin na musamman kan Korea ta Arewa.

A cikin watan Julin da ya gabata ne, Korea Ta Arewa ta harba makamai biyu masu linzami tare da fadin cewa, tana da karfin da za ta iya kai farmaki a dukkanin sassan Amurka.

Kasashen duniya da suka hada da Korea ta Kudu da Japan da Amurka da sun soki matakin gwaje-gwajen.

Daga cikin abubuwan da Korea ta Arewa ke fitar wa zuwa China akwai tama da karfe da kuma gawayi, abin da ke taka rawa dangane da kudaden shiga da take samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.