Isa ga babban shafi
Amurka

An kafa dokar hana fita a Houston da ke fama da ambaliya

Hukumomin Houston a Amurka sun kafa dokar hana fitar dare domin magance matsalar satar kayan jama’a da ake samu sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan agaji.

'Yan gudun hijirar ambaliyar ruwa a Houston na Amurka
'Yan gudun hijirar ambaliyar ruwa a Houston na Amurka AFP/Joe Raedle
Talla

Magajin Garin Houston Sylvester Turner ya sanar da kafa dokar hana fitar daren da zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba.

Turner ya ce suna da dubban mutanen da suka bar gidajen su domin samun mafaka a sansanonin da aka tanada, amma bata-gari na amfani da damar wajen fasa gidajen mutane.

Shugaban ‘Yan Sandan birnin Art Acevedo ya ce shi ya bada shawarar sanya dokar saboda rahotanni da suka samu na satar da ake yi wa jama’a.

Shugaba Donald Trump da ya zagaya sassan Jihar Texas ya yabawa masu aikin agaji wadanda ke ci gaba da taimakawa jama’a.

Fadar shugaban ta ce Trump zai sake komawa Yankin ranar Asabar domin ganin halin da ake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.