Guguwa mai gudun kilomita 195 a sa'a guda ta afkawa Texas
Mahaukaciyar Guguwa mai karfin gaske, ta afkawa jihar Texas da ke Amurka, wadda masana suka bayyana ta a matsayin babbar masifa ga jihar da ma makwabtanta.
Wallafawa ranar:
Guguwar mai tafiyar kilomita 195 a sa’a guda, da masana suka yi wa lakabi da Huriccane Harvey, ana sa ran ta zama mafi karfin wadda ta taba afkawa Amurka tun bayan makamancin hakan a shekarar 2005.
Tun kafin guguwar ta isa jihar, shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan takardar ayyana Texas a matsayin jihar da ke fuskantar masifa, tare da bada umarnin fitar da kudaden kai agaji.
An dai samu katsewar wutar lantarki a mafi yawancin sassan jihar, yayin da guguwar ke tunkarota, kuma ana sa rana ta juye ruwan sama kan ma’aunin Senti mita 89 tsawon kwani hudu zuwa biyar a sassan jihar ta Texas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu