Isa ga babban shafi
Amurka

Ana fargabar samun fashewa a Houston mai fama da ambaliya

Masu aikin agaji a Jihar Texas ta Amurka sun sanar da samo gawawakin wasu mutane 6 iyalan gida guda, yayin da yanzu haka ake fargabar fashewar wani kamfanin hada sinadari mai guba kusa da Houston.

Mutane sama da miliyan ambaliya ta tursasawa barin gidajensu a Houston da Texas
Mutane sama da miliyan ambaliya ta tursasawa barin gidajensu a Houston da Texas REUTERS/Adrees Latif
Talla

Tuni aka umurci mutanen da ke zama kusa da kamfanin da su fice daga gidajensu domin kaucewa duk wani hadari.

Wannan na zuwa ne bayan sake samu karuwar ruwan sama a Yankin.

Ruwan sama mai karfin gaske ya sake dawowa a yankin Texas bayan fama da ruwan saman a tsawon kwanaki biyar, inda ya kara haddasa cikas ga masu ayyukan ceton.

Ambaliyar ruwan ta samo asali ne daga mahaukaciyar guguwar nan mai suna Harvey.

A wannan karo dai guguwar ta fi shafar gagaruwan da ke gabar ruwan gabashin Amurka ne, kuma birnin Houston na jihar Texas da kuma Louisiana da ke Orleans, na daga cikin wadanda ambaliyar ta fi yin mumman ta’adi.

Duk da cewa kawo yanzu ba wasu cikakkun alkalumma dangane da adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan lamari, da ke gaf da share tsawon mako daya, amma kafafen yada labarai na Amurka na cewa adadin mamatan zai kai 30.

Akwai mutane kusan miliyan daya da suka bar gidajensu, yayin da wasu da dama suka makale a wasu yankuna sakamakon yadda ruwa ya yanke hanyoyin mota da turakun wutar lantarki da na wayar tarho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.