Isa ga babban shafi
Amurka

Yiyuwar sake bitar dokar mallakar bindiga a Amurka

Harin da dan bindiga ya kai tare da kashe mutane 59 a wani otel da ke Las Vegas na kasar Amurka, ga alama zai bayar da damar zaunawa domin yi wa dokar mallakar makamai a kasar gyara.

Ginin otel na Las Vegas, Inda dan bindiga Stephen Paddock ya yi barin wuta har ya kashe mutane 59
Ginin otel na Las Vegas, Inda dan bindiga Stephen Paddock ya yi barin wuta har ya kashe mutane 59 David Becker/GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP
Talla

Bayanai na nuni da cewa, yanzu haka jam’iyyar Republican da kuma masu kamfanonin kera bindigogi na gaf da cimma jituwa kan wannan batu, lamarin da zai bai wa majalisar dokoki damar tattaunawa kan yadda za a yi wa tsarin bai wa jama’a damar mallakar makamai gyaran fuska.

Bayanai na nuni da cewa irin bindigogin da dan bindigar ya yi amfani da su wajen kai wannan hari, bindigogi ne da ka kara ingantawa a baya-baya nan, lamarin da kuma ke kara jefa fargaba a cikin zukatan Amurkawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.