Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya tabbatar da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da matsayin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, a wani jawabi da ya sauya manufofin Amurka wanda ake ganin zai iya haifar da tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Shugaban kasar Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaba Trump ya ce Isra'ila kasa ce mai ‘yanci saboda haka tana iya sanya babban birnin ta inda ta ke so.

Trump ya ce matakin ba zai sauya matsayin Amurka na samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba idan sun amince a tsakanin su.

Tuni wannan batu na Mista Trump ya janyo suka daga shugabannin duniya daban-daban.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka, inda ya ke cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar.

Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke ziyarar Algeria ya bayyana matakin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci kaucewa tashin hankali.

Ita kuwa kungiyar Hamas ta bayyana matakin a matsayin abinda zai bude kofar jahannama ga muradun Amurka.

Ismail Ridwan da ke Magana da yawun kungiyar ya bukaci taron kungiyar kasashen larabawa da na Musulmai domin katse hulda da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.