Aman-wutan dutse ya tilastawa Dubban mutane barin gidajensu a Philippines
Akalla Mutum dubu 90 ne suka tserewa rayukansu sakamakon aman-wutan dutse da ke barazanar a wasu yankunan Philippines, lamarin da mahukunta kasar ke cewar ya tsananta rashin tsafta a wuraren da mutanen ke samun mafaka.
Wallafawa ranar:
Makonnin biyu kenan da kasar ta fara fuskantar iftila’I aman wutan dutsen, lamarin da ya tursasawa mahukunta kasar umartan mazauna kusa da tsaunin Mayon su nesanta kansu da akalla kilomita 5.6 daga tsaunin.
Wannan dalili ya sanya mutane da dama tururuwa zuwa yankunan tsira, lamarin da ya tsananta rashin tsafta saboda yawan mutane da suka taru a wuri guda.
A cewar Gwamnan lardin Albay, Al Franncis Bichara, mutane da aka bai wa mafaka a sansanonin za su bukaci akalla wata guda kafin su koma yankunansu.
Sai dai ya yi gargadi karancin kayayyakin tallafi, da kuma rashin mekewaye a matsugunan, inda ya ce mutum 200 na amfani da wuri guda wajen bahaya, alhalin ana bukatar bundakunan 1,222 domin amfani kowani mutum 50 a sansanin.
Shugaban Kasar Rodrigo Duterte da ya kai ziyarci yankin domin ganin halin da mutane ke ciki, ya nuna damuwarsa kan rashin mekewayen.
Wannan shine karo na 52 a cikin karni 4 da tsaunin Mayon da ke da tsayin Kilomita 330 a kudu maso gabashin Manila ke aman wuta. A shekara ta 1814 irin wannan iftila'in ya kashe mutum 1,200 lokacin da ya lulube garin Cagsawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu