Amurka za ta hukunta wanda ake zargi da kai harin guba a Syria
Shugaba Donald Trump na Amurka yayi gargadin daukan tsatstsaurar mataki muddin aka gano cewa da gaske ne an yi amfani da makamai masu guba a wani hari da aka kai garin Douma na kasar Syria.
Wallafawa ranar:
Kasashen duniya da dama dai sun nuna rashin jin dadin rahotanni dake nuna anyi amfani da makamai masu guba jim kadan bayan da ‘yan tawaye suka amince su bar garin Douma, wanda shi ne gari dake hannunsu na karshe.
Barazanar shugaba Trump na zuwa ne shekara daya chur da Amurka da chilla wani makami mai linzami sararin samaniyar Syria don maida martani game da harin makami mai guba na Sarin da aka kai kan fararen hula.
A sakon Trump na baya-bayan nan na cewa akwai mamata da yawa da suka hada da mata da yara kanana sakamakon hari da makamai masu guba a Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu