Mike Pence na ziyara a Brazil kan kwararowar 'Yan cirani Amurka
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya isa kasar Brazil yau Talata don tattaunawa da shugaba Michel Temer kan batutuwan da suka shafi kwararowar ‘yan ci rani dama rikicin kasuwancin baya-bayan nan.
Wallafawa ranar:
Wannan shi ne karon farko da wani mai fada aji daga gwamnatin ta Amurka ke kai ziyara Brazil tun bayan hawan mulkin Donald Trump.
Wani jigo a tawagar ta Pence ya shidawa manema labarai cewa batun ‘yan cirani shi ne makasudin ziyarar yayinda batun kamfaonin karafa da samfoli mallakin Brazil zai biyo baya.
Gwamnatin Trump dai ta fuskanci mummunar suka daga Brazil dama sauran kasashen duniya bayan da ta raba akalla ‘ya’yan ‘yan ciranin dubu 2 da dari biyar da iyayensu saboda sun shiga kasar ba bisa ka’ida ba ciki kuwa har da iyalai 50 ‘yan asalin kasar Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu