Isa ga babban shafi

Duterte zai kara tsananta yaki da miyagun kwayoyi

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte ya sha alwashin ci gaba da yaki da shan miyagun kwayoyi wanda ya hallaka dubban jama’a a kasar. Duterte wanda ke wannan batu yayin jawabin shekara-shekara kan halin da kasar ke ciki ya ce za su dora kan kokarin da su ke na ganin sun kawar da dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Jawaban na Shugaba Duterte dai ya zo da tasgaro musamman bayan da wasu taron masu zanga-zanga suka cika titunan kasar tare da neman samar da sauye-sauye a tsare-tsaren gwamnatinsa.
Jawaban na Shugaba Duterte dai ya zo da tasgaro musamman bayan da wasu taron masu zanga-zanga suka cika titunan kasar tare da neman samar da sauye-sauye a tsare-tsaren gwamnatinsa. REUTERS/Romeo Ranoco
Talla

Shekara ta uku kenan da shugaba Duterte ya kaddamar da yaki da miyagun kwayoyi a kasar wadda ke tafka asarar jama’a sanadiyyar dabi’ar ta shan miyagun kwayoyi bayan fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan bukatar kawo karshen matsalar.

Rahotanni sun ce tun bayan kaddamar da yakin kan sha da safarar miyagun kwayoyi a shekarar 2016 bayan hawa mulkin shugaba Duterte, akalla mutane dubu 4 da 354 aka hallaka bayan kama su da safarar miyagun kwayoyin.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi ikirarin cewa adadin mutanen da aka hallaka sanadiyyar fataucin kwayoyin ya haura linki biyu kan wanda gwamnatin ta Phillippines ta sanar, matakin da suka ce ya zama take hakkin bil’adama.

Jawaban na Shugaba Duterte dai ya zo da tasgaro musamman bayan da wasu taron masu zanga-zanga suka cika titunan kasar tare da neman samar da sauye-sauye a tsare-tsaren gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.