Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Trump ya nemi ganawa da shugabannin Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar a shirye yake ya gana da shugabannin Iran duk lokacin da suke so, ba tare da gindaya sharadodi ba.

A makon jiya, jami’an kasar Iran sun bayyana cewar sau 8 shugaba Trump ke bukatar ganawa da shugaba Hassan Rouhani lokacin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya amma shugaban na Iran na hawa kujerar naki.
A makon jiya, jami’an kasar Iran sun bayyana cewar sau 8 shugaba Trump ke bukatar ganawa da shugaba Hassan Rouhani lokacin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya amma shugaban na Iran na hawa kujerar naki. REUTERS/Carlos Barria
Talla

Trump wanda ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai tare da Firaministan Italia Guiseppe Conte ya ce zai gana da shugabannin Iran muddin suna bukatar haka.

Wannan sauyin matsayi na zuwa ne kasa da mako guda bayan shugaba Trump ya gargadi shugaban Iran Hassan Rouhani cewar muddin suka cigaba da yiwa Amurka barazana za su gamu da fushin da ba su taba gani ba a tarihin duniya.

Tun kafin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka ya soki yarjejeniyar nukiliyar da Amurka tare da kasashen duniya suka kulla da Iran, yayin da ya yi watsi da shirin bayan ya hau karagar mulki.

A makon jiya, jami’an kasar Iran sun bayyana cewar sau 8 shugaba Trump ke bukatar ganawa da shugaba Hassan Rouhani lokacin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya amma shugaban na Iran na hawa kujerar naki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.