Isa ga babban shafi
Yemen

MDD tace dukkanin bangarorin dake rikici a Yemen sun aikata laifuka yaki

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce dukkannin bangarorin da ke da hannu a rikici a kasar Yemen sun aikata laifuffukan yaki.Wannan zargi dai na kunshe ne a cikin wani rahoto da masu binciken suka fitar ranar Talata 28 ga watan Ogustan 2018, inda suka ce, suna da tabbacin cewa bangarorin biyu dake yaki a Yaman sun take duk dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama.

kaburburan yaran da suka rasa rayukansu sakamakon harin  jiragen sama da dakarun hadakar kasashen larabawa a ranar 9 ga watan ogustan  2018
kaburburan yaran da suka rasa rayukansu sakamakon harin jiragen sama da dakarun hadakar kasashen larabawa a ranar 9 ga watan ogustan 2018 REUTERS/Naif Rahma
Talla

Kamel Jendoubi, wanda ya jagoranci komitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniyar wajen gudanar da bincike kan yakin kasar ta Yaman, ya ce cin zarafin da bangarorin biyu ‘yan tawayen huti da kuma dakarun rundunar hadakar kasashen larabawa da kasar Saudiya ke jagoranta, na zama aikata manyan laifukan yaki.

Cikin laifukan da rahoton wanda ya fito a karon farko ya zayyana, sun hada da kai hare-ren jiragen sama kan fararen hula, amfani da ‘yan kasa da shekaru 18 a aikin soja, sauran laifukan sun hada da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, da fyade da kuma azaftarwa.

Mista Jendoubi, ya ce suna da kwararan shaidu da ke tabbatar da hakan, bugu da kari ma, za a gabatar da jerin sunayen wasu mutane da ake zargi ga babban Kwamishinan kare hakkin bil-adama na Majalisar Dinkin Duniya a yau litanin 28 ga watan ogusta 2018.

Rikicin kasar Yemen dai, ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane dubu goma tun cikin watan Maris din shekarar 2015, lokacin dakarun hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta ‘yan Sunni, suka shiga kasar domin yakar 'yan tawaye Huthi yan shi’a, wajen hanasu kawar da gwamnatin shugaba Mansour Hadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.