Isa ga babban shafi
Birtaniya-Afrika

May ta sha alwashin karfafa alaka da Kenya bayan ficewa daga EU

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sha alwashin karfafa alakar kasuwanci tsakaninta da Kasar Kenya bayan kammala ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai nan da watanni 7 masu zuwa.

Bayan kammala ganawar shugaba Kenyatta ya shaida cewa May ta tabbatar masa da dorewar kasuwanci dama bunkasa shi bayan ficewarta daga kungiyar ta EU.
Bayan kammala ganawar shugaba Kenyatta ya shaida cewa May ta tabbatar masa da dorewar kasuwanci dama bunkasa shi bayan ficewarta daga kungiyar ta EU. Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Theresa May wadda ke sanar da hakan a ganawarta da shugaba Uhuru Kenyatta yayin ziyarar aiki ta kwanaki 3 da yanzu haka ta ke gudanarwa a nahiyar Afrika ta ce bayan kammala ficewar kasar ta kungiyar tarayyar Turai EU za ta mayar da hankali ne wajen gudanar da kasuwanci kai tsaye da kasashen Afrika musamman Kenya.

Ziyarar ta May zuwa Kenya ita ce irinta ta farko da Firaministan Birtaniya ke kai wa kasar cikin shekaru 30, inda suka shafe kusan sa'o'i 2 suna ganawa tsakaninta da Kenyatta.

May ta tabbatar da cewa baya ga batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kasuwanci Birtaniyar za kuma ta tallafawa Kenyar ta fuskar yaki da karancin tsaro baya ga yakar cin hanci da rashawa.

Bayan kammala ganawar shugaba Kenyatta ya shaida cewa May ta tabbatar masa da dorewar kasuwanci dama bunkasa shi bayan ficewarta daga kungiyar ta EU.

Ganawar ta Kenyatta da May na zuwa ne kwanaki kalilan bayan dawowarsa daga Amurka inda ya gana da Donald Trump yayinda kuma ya ke shirin tafiya taron koli kan kasuwanci tsakanin Africa da China.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.