Faransa-Birtaniya
Ganawar Emmanuel Macron da Theresa May
Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a ranar farko ta hutun da ya fara a wannan juma’a, ya gana da firaministar Birtaniya Theresa May inda bayanai ke cewa sun tattauna kan batun ficewar Birtaniya daga gungun Tarayyar Turai.
Wallafawa ranar:
Talla
An yi ganawar ce a Brégançon da kudu maso gabashin Faransa, inda shugaban ke hutunsa na karshen damina.
Ita ma Firaminista May, na wannan ziyara a Faransa ce kwana daya bayan ta kammala nata hutun a kasar Italiya, to sai dai ba wasu cikakkun bayanai dangane da abin da mutanen biyu suka tattauna a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu