Isa ga babban shafi
Birtaniya

Theresa ta rasa rinjaje a zauren Majalisar Birtaniya

Sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar jiyar alhamis a kasar Birtaniya, na nuni da cewa jam’iyyar masu ra’ayin rikau a karkashin jagorancin Theresa ce ke sahun gaba, duk da cewa jam’iyyar ta rasa rinjaye a zauren majalisar.

Theresa May, Firaministar Birtaniya
Theresa May, Firaministar Birtaniya REUTERS
Talla

Sakamakon dai na nuni da cewa jam’iyyar ta Theresa May ta samu kujeru 309 ne daga cikin 650 da ake da su a zauren majalisar ta Birtaniya, wanda babban koma-baya ne ga jam’iyyar wadda ke da kujeru 330a majalisar da ke gaf da kawo karshen wa’adin aikinta, yayin da jam’iyyar kwadago a karkashin jagorancin Jeremy Corbyn ta tashi da kujeru 266.

Babban fatan Theresa da magoya bayanta dangane da wannan zabe dai shi ne samun cikakken rinjaye a majalisar ba tare da ta nemi kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa ba, kuma ta haka ne wadanda suka jagoranci gwagwarmayar ballewar kasar daga Turai za su iya aiwatar da manufofinsu a siyasance.

Jam’iyyar kwadago wadda ke matsayin babbar jam’iyyar adawa a Birtaniya, ta lashe kujeru 266, kuma hakan gagarumar nasara ce ga Jeremy Corbyn lura da cewa a karkashin jagoranci tsohon shugabanta Ed Miliband jam’iyyar na da kujeru 232 ne a zauren majalisar.

Duk da wannan sakamako, Theresa May za ta iya samun damar ci gaba da kasasncewa Firaminstar kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.