Mahaukaciyar guguwa na dab da afka wa Philippines
Mutane miliyan biyar a Philippines na fuskantar barazanar mahaukaciyar guguwar "Mangkhut" da ke gudun kilomita 255 a cikin sa’a guda.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na cewa, yanzu haka guguwar na tattaro iska kafin ta afka wa yankin arewacin tsibirin Luzon a gobe Asabar.
Tuni aka soke zirga-zirgar jiragen sama da rufe makarantu, yayin da sojoji ke cikin shirin bada agajin gaggawa.
Hukumomin kasar sun gargadi cewa, da yiwuwar guguwar mai tafe da ruwan sama ta haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar laka.
Kasar Philippines na shiga cikin mawuyacin hali da zaran guguwa ta afka ma ta, in da a shekarar 2013, ibtila’in ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 7 tare da jefa miliyoyi cikin kunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu