Iska da Goguwa ta kashe mutane biyu a Philippines
Wata mahaukaciyar guguwa dauke da ruwan sama mai karfin gaske da ake kira Super Typhoon Mangkhut ta dira a kasar Philippines, a yau Asabar inda ta fara da hallaka mutane takwas.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yankin data dira dake arewacin tsubirin Luzom, ya kasance yanki ne dake da mutane akalla miliyan 10 wadanda yawanci ke zaune a gidaje da aka yi da katako.
Majiyoyin samun labarai sun ce, yanzu haka a yankin babu hasken wutan lantarki, itatuwa sai faduwa suke yi, a yayin da rufin gidaje ke kwarewa.
tuni dai kungiyar agaji ta Handicap International, ta aika da tawagar masu aikin jinkai domin taimakawa a kasar Philippines, tare da yin kiran masu bada taimako, su taimakawa al’umar da suka samu kansu cikin hali, sakamakon mahaukaciyar guguwar dake dauke da ruwan saman da ta rutsa da su.
guguwar dai ta kasance mafi karfi dake gudun 255 a awa da ta shafi tsibirin na Philippines a wannan shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu