Isa ga babban shafi
Indonesia

Mutane dubu 200 na bukatar agajin gaggawa a Indonesia

Kasar Indonesiya ta bukaci kasashen duniya su taimaka ma ta domin shawo kan matsalar ayyukan jinkai da suka yi kamari sakamakon girgizar kasa da ta haddasa ambaliyar teku ta tsunami, in da sama da mutane dubu 200 ke bukatar agajin gaggawa.

Wasu daga cikin masu neman agaji sakamakon aukuwar ibtila'in girgizar kasa a Indonesia
Wasu daga cikin masu neman agaji sakamakon aukuwar ibtila'in girgizar kasa a Indonesia Antara Foto/Rolex Malaha via REUTERS
Talla

Ibtila'in ya tilasta wa shugaban kasar, Joko Widodo mika hannu neman taimakon kasashen duniya, in da yanzu haka kasashe 18 hade da wasu kungiyoyin agaji na duniya da dama suka nuna sha’ar taimakawa.

Ministan Tsaron Kasar Janar Wiranto ya ce, kamar yadda ya zama al’ada a tsakanin kasashen duniya na neman taimako idan an shiga cikin irin wannan hali da ita ma Indnesia ta taba taimakawa a wani bangaren, a halin yanzu tana bukatar a taimaka ma ta a cikin halin da ta samu kanta a ciki.

Ofishin Hukumar Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya, ya kiyasta yawan mutanen da ke cikin mawuyacin hali kuma suke bukatar taimakon gaggawa da cewa sun kai dubu 191a Indonesia.

Ibtila'in ya tilasta wa akalla mutane dubu 59 kaurace wa kasar, yayin da mutane kimanin dubu daya suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.