Isa ga babban shafi
MDD

Rahoto kan tsanantar yunwa a sassan duniya

Rahoton binciken da wasu kungiyoyi masu zamnan kansu suka gudanar na nuni da cewa yanzu haka akwai kasashe akalla 60 da jama’a ke fama da matsananciyar yunwa a sassan duniya.

Jacques Diouf, daraktan hukumar abinci da noma ta duniya FAO
Jacques Diouf, daraktan hukumar abinci da noma ta duniya FAO (Photo : FAO/Guilio Napolitano)
Talla

Rahoton wanda kungiyar Concern Worldwide ta kasar Ireland da Welt-hungerhilfe ta kasar Jamus suka tsara, an fitar da shi ne a birnin Rome daidai lokacin ake fara babban taron Hukumar Abinci da Noma ta MDD wato FOA.

 

Rahoton ya bayyana cewa kasashen Chadi, Yemen, Madagascar, Zambia da kuma Sierra Leone ne suka fi fama da matsananciyar yunwar yanzu haka, yayin da Somalia, Burundi da kuma Syria ke a  cikin rukunin kasashen da yunwar ta ddaba amma a mataki na biyu.

 

Adadin wadanda ke cikin hali na bukatar samun tallafin abinci a gaggauce kuwa sun kai milyan 124 a cewar rahoton, yayin da wasu yara kanana sama da milyan 151 ke fama da karancin abinci mai gina jiki a sassan duniya.

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kawai adadin yara da ke fama da rashin abinci mai gina jiki ya kai 61,8%, sai Somalia 50,6% yayin  da a Zimbabwe adadinsu ya kai 46,6%.

To sai dai rahoton ya ce an samu gagarumin cigaba ta fannin inganta rayuwar jama’a sakamakon samun isassashen abinci a kasashen Angola, Habasha, Rwanda Sri Lanka da kuma Bangladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.