Isa ga babban shafi
Khashoggi-Turkiya

Kungiyar 'Yan jaridu mazauna Turkiya ta nemi adalci a kisan Khashoggi

Wata kungiyar ‘yan jaridu mazauna Turkiyya da ake kira TAM ta bukaci hukunta wadanda ke da hannu a kisan fitaccen dan jaridar Saudiyyar nan Jamal Khashoggi da aka hallaka a ofishin jakadancin Saudin da ke birnin Santambul farkon watan nan.

Kungiyar ta TAM ta nemi lallai a hukunta duk wanda ke da hannu a kisan fitaccen dan jaridar tare da jami'an ofishin jakadancin su 18.
Kungiyar ta TAM ta nemi lallai a hukunta duk wanda ke da hannu a kisan fitaccen dan jaridar tare da jami'an ofishin jakadancin su 18. ©REUTERS/Murad Sezer
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar jim kadan bayan tabbacin da saudiyya ta fitar na amincewa da kisan fitaccen dan jaridar a yau Asabar, kungiyar ta TAM wadda Khashoggi mamba ne a cikinta, ta ce ba wai mutane 18 da suka hadu wajen kisan fitaccen dan jaridar ba, har ma da sauran wadanda ke da hannu ko a ina su ke.

Matakin kungiyar na zuwa bayan da Saudiyyar ta sanar da kame wasu jami'an ofishin su 18 baya ga tube shugabansu game da kisan na Khashoggi wanda mahukuntan suka ce ya rasa ransa ne bayan fadan da ya kaure tsakaninsa da Jami'an.

An dai shafe tsawon lokaci ana neman Jamal Khashoggi dan jarida da ya yi kaurin suna wajen sukar tsarin masarautar saudiyya wanda da farko aka sanar da bacewarsa ko da dai akwai bayanai da ke nuna cewa an kashe shi ne sa'o'i kalilan bayan shigarsa Ofishin jakadancin ranar 2 ga watan nan na Oktoba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.