Trump ya ce yana sanya idanu kan zanga-zangar Faransa
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana ci gaba da sa ido kan zanga zangar da ke gudana a Faransa, a wani yunkuri na sake fito da barakar da ke tsakaninsa da shugaba Emmanuel Macron.
Wallafawa ranar:
A sakon da ya aike ta kafar twitter, Trump ya bayyana cewar zanga zangar da tashin hankalin da ake samu ba su da nasaba da yadda aka ci zarafin Amurka wajen yarjejeniyar kasuwanci da kasashen Turai da kuma biyan kudin tsaro domin kariya.
Trump ya ce ya zama dole a sake gyara wadannan batutuwa guda biyu cikin gaggawa.
Akalla mutane 130 aka kama bayan zanga zangar ranar asabar da ta haifar da tashin hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu