Isa ga babban shafi
Venezuela

Tilas kasashe su bayyana matsayinsu kan rikicin Venezuela - Amurka

Amurka ta bukaci kasashen duniya, su gaggauta bayyana matsayinsu kan rikicin siyasar Venezuela, inda jagoran ‘yan adawar kasar Juan Guaido ya sanar da kafa sabuwar gwamnati, da nufin kawo karshen mulkin Nicolas Maduro, wanda ya bayyana a matsayin haramtacce.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. ©REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Amurka ta bukaci hakan ne yayin zaman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya na jiya Asabar kan kasar ta Venezuela. Sai dai Rasha ta hau kujerar naki, tare da zargin Amurka da yunkurin yiwa gwamnatin Nicolas Maduro juyin mulkin.

Yayin zaman kwamitin tsaron dai, Ministan harkokin wajen Venezuela Jorge Arreaza ya yi watsi da wa’adin da kungiyar Tarayyar Turai EU ta baiwa gwamnatinsu, na gudanar da sabon zaben shugaban kasa nan da kwanaki 8, ko kuma sun amince da sabuwar gwamnatin Juan Guaido.

A farkon makon jiya jagoran ‘yan adawar Venezuela kuma shugaban majalisar dokokin kasar, Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaba, matakin da ya samu goyon bayan shugaba Donald Trump da sauran kasashen Latin na yankin Kudancin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.