Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na jan hankulan kasashen duniya kan dumamar yanayi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, yana fatan taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya G20, zai mayar da hankali kan matsalar dumamar yanayi da yanzu haka ke ci gaba da yi wa duniya barazana tare da fatan taron zai fitar da wani tsari na bai-daya domin tunkarar wannan matsala.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Koji Sasahara/Pool via REUTERS
Talla

Macron wanda ke gabatar da taron manema labarai na hadin-gwiwa da Firaministan Japan Shinzo Abe a birnin Tokyo a yau laraba, ya ce a fili take cewa dumamar yanayi na haifar da mummunar illa, saboda haka ya zama wajibi taron na G20 ya fitar da gargadi a matsayin iyakar da bai kamata duniya ta tsallaka ba.

Har ila yau shugaba Macron ya ce, wani abu da ya kamata taron ya mayar da hankali shi ne rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China, wanda ya ce, yana shafar sha’anin kasuwanci a duniya.

Wasu batutuwa da shugabannin biyu suka tattauna a ganawarsu sun hada da makomar tubabben shugaban kamfanin kera motoci na Nissan-Renault da Mitsubishi Carlos Ghosn dan kasar Faransa, yayinda taron na G20 zai gudana a wani yanayi da ake fargabar barkewar rikicin tsakanin Iran da Amurka da kuma kawayenta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.