Isa ga babban shafi
Facebook-Australia

Facebook ta katse hanyoyin sadarwar shafukan labarai a Australia

Matakin kamfanin Facebook na katse damar isa ga shafukan labarai a Austarila ya jefa jama’a cikin fargabar yiwuwar yaduwar labaran karya su mamaye shafukan sada zumunta.

Facebook da Google sun katse layukan sadarwa a Australia.
Facebook da Google sun katse layukan sadarwa a Australia. AFP/File
Talla

Da safiyar yau Alhamis ne al’ummar Australia suka wayi gari da katsewar shafukan labarai ta yadda basa iya shiga kama daga shafukan cikin kasar har ma dana ketare don samun wadattun labarai, yayinda shafukan labaran kasar gabaki daya ya bace daga kan Google.

Matakin kamfanin na Facebook wanda ake ganin yana da alaka da yunkurin gwamnati na tilastawa kamfanin da shi da Google biyan shafukan labarai ladan labaransu da ake iya karantawa ta shafukan, tuni ya haddasa bacin rai daga al’ummar kasar wadanda suka gaza samun sukunin shiga shafukan duniya baki daya.

Manyan shafukan gwamnati da ke wallafa matakan gaggawa na kariya kan Covid-19 da gobarar daji da ambaliyar ruwa da kuma guguwa dukkaninsu sun gaza wallafe-wallafe bare akai ga karanta abinda suka wallafa a shafukan, ko da ya ke tuni kamfanin na Facebook ya gyara matsalar da aka fuskanta yayinda suka dawo bakin aiki.

Tuni dai masu wallafe-wallafen karya suka yi amfani da damar wajen baza hajojinsu, ko da ya ke shafukan sadarwa da dama sun yi saurin wallafa gargadi kan yiwuwar samun bazuwar labaran karyar gabanin Facebook ya dawo da shafukan wadanda a farko suka dauke gabaki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.