Isa ga babban shafi
Coronavirus - Turai

EU zata tallafawa kasashe malauta da allurar rigakafin korona miliyan 100

Kungiyar tarayyar Turai zata bada tallafin alluran rigakafin Corona guda miliyan 100 ga kasashe matalauta a wani bangare na kokarin ganin an tsamo al’ummar duniya daga bala’in annobar Coronavirus, da kuma magance sake barkewar ta.

Framministan Italiya Mario Draghi tare da shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, a Roma, ranar 21 ga watan Mayan 2021
Framministan Italiya Mario Draghi tare da shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, a Roma, ranar 21 ga watan Mayan 2021 AFP - TIZIANA FABI
Talla

Shugabar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula Von Der Leyen da kuma Prime Ministan Italiya Mario Draghi wanda shine ke jagorantar taron kungiyar kasashen G20 ne suka bada wannan sanarwa.

Ana sa ran kasashen duniya zasu yi amfani da taron G20 din wajen sake jadadda muhimmancin da ke akwai  na yaki da cutar Coronavirus ta hanyar tallafawa kasashen da bazasu iya samarwa kansu da allurar rigakafin cutar ba.

Kashen duniya sunyi sakaci

Tace barkewar annobar Corona ta nuna karara yadda kasashen duniya suka yi sakaci da shirin ko ta kwana na tunkarar irin wannan annoba, la’akari da yadda ta gigita kasashen duniya manya da kanana.

Tace a don haka akwai bukatar sake hada kai don aiki tare wajen yaki da cutar da kuma amfani da sauran hanyoyin fasaha wajen gano maganin ta cikin gaggawa.

Annobar korona ta zowa duniya ta bazata

Annobar Corona dai ta zowa duniya ne a bazata kuma a lokacin da ba’a shirya faruwar makamanciyar wannan annoba da zata zagaye duniya haka ba, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.