Isa ga babban shafi
Fafaroma-Vatican

Fafaroma ya samar da gyara ga kundin hukunta masu laifi na Vatican

Shugaban darikar Katlika na Duniya Fafaroma Francis ya samar da sabbin sauye sauye a dokar hukunta manyan laifuka na Vatican ta hanyar shigar da hukunce hukunce masu tsauri kan malaman majami’ar da ake samu da laifukan cin zarafi ko aikata badala kan mata da kananan yara a sassan Duniya.

Shugaban darikar Katlika na Duniya Fafaroma Francis.
Shugaban darikar Katlika na Duniya Fafaroma Francis. REUTERS - POOL
Talla

Sabbin sauye sauyen ga kundin hukunta masu laifi na Vatican na da nufin tsaurara dokoki da kuma hukunta malaman majami’ar da aka samu da laifin bata yara ko kuma cin zarafin mata ta hanyar lalata, zarge-zargen da ke kara yawaita kan malaman darikar ta Katlika a sassan Duniya.

Tun bayan karbar ragamar shugabancin darikar Katlika ta Duniyar a 2013, Fafaroma Francis dan Argentina ya ke kokarin samar da sauye-sauye don dakile cin zarafi ta hanyar lalatar da yara ke fuskanta, wanda ke fuskantar caccaka musamman daga kungiyoyin kare hakkin dan adam.

A cewar Fafaroma, manufar samar da sauye-sauyen karon farko tun bayan 1983, shi ne tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta da kuma dakile faruwar makamantan laifukan a nan gaba da ma  dawo da aminci da martabar malaman majami’ar ko’ina a Duniya.

Ko a shekarar 2019, Fafaroma yayin wani babban taro ga yadda malaman majami’a kan cin zarafin mata ta hanyar lalata, sai da jagoran ya samar da wasu dokoki kebantattu da suka kai ga gudanar da bincike da wadanda ake zargi da aikata badalar.

Sabbin sauye sauyen na Fafaroma ga kundin hukunta masu laifi na fadar Vatican da zai fara aiki daga watan Disamba mai zuwa ya tabbatar da kima da kuma mutunci kowanne jinsi imma tsiraru ko kuma masu rinjaye, yayinda ya sanar da manyan hukunci kan wadanda suka aikata makamantan laifukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.