Isa ga babban shafi
Bakin Haure

Fafaroma Francis ya cacaki kasashen duniya kan 'yan ci-rani

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Franccis ya koma tsibirin Lebos da ta kasance matattarar farko ta bakin-haure a Turai da ya ziyarta a shekarar 2016, inda ya ce, yin watsi da halin da bakin ke ciki tamkar rashin wayewa ne.

Faforoma Francis lokacin da ya gana da 'yan gudun hijira a tsibirin Lisbos 05/12/21.
Faforoma Francis lokacin da ya gana da 'yan gudun hijira a tsibirin Lisbos 05/12/21. Andreas SOLARO AFP
Talla

Fafaroma ya jima yana tsokaci kan mawuyacin halin da bakin-haure ke ciki, kuma ziyararsa a tsibirin na Lesbos na zuwa ne kwana guda da ya gabatar da wata makala, inda a cikinta ya caccaki kasashen Turai da ya ce, muguwar akidar nan ta son-kai ta rarraba kawunansu.

Faforoma Francis lokacin da ya gana da 'yan gudun hijira a tsibirin Lisbos 05/12/21.
Faforoma Francis lokacin da ya gana da 'yan gudun hijira a tsibirin Lisbos 05/12/21. via REUTERS - VATICAN MEDIA

Fafaroman wanda ya shafe tsawon sa’o’i biyu a sansanin ‘yan gudun hijira na Mavrouvouni mai dauke da mutane kusan dubu 2 da 200 a Lesbos, ya ce, akwai wasu mutane a nahiyar Turai da suka tsaya kai da fata domin ganin matsalar ta ci gaba da girmama saboda ba ta shafe su ba.

A rana ta biyu ta ziyarasa a Girka, Fafaroman ya gana da kananan yaran ‘yan gudun hijira da kuma danginsu, inda har ya tsaya tare da rungumar wani karamin yaro mai suna Mustafa.

Shugaban Katolikan ya shaida wa masu neman mafakar cewa, ina kokarin ganin na taimake ku, yayin da mutane suka yi cincirindo a wani dakin shema domin rera waka ga Fafaroman.

Faforoma Francis yayin ziyara a Cypros.
Faforoma Francis yayin ziyara a Cypros. Andreas SOLARO AFP

Kazalika shugaban addinin ya yi gargadin cewa, tekun Mediterreanean na ci gaba da zama kushewa mara alama saboda yadda bakin-hauren ke rasa rayukansu a cikin tekun.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.