Isa ga babban shafi
SAKIN-AURE

Kotu ta umurci jagoran Dubai biyan tsohuwar matar sa Dala miliyan 730

Wata Kotu a birnin London ta umurci jagoran Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum da ya biya tsohuwar matar sa da yaran sa guda biyu Fam miliyan 550 ko kuma Dala miliyan 730 a matsayin kudin sallama a shari’ar raba auran su da aka kammala yau a Birtaniya.

Gimbiya Haya bint Al-Hussein da mijinta, Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum, a ranar 17 ga Yuni na shekarar 2010.
Gimbiya Haya bint Al-Hussein da mijinta, Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum, a ranar 17 ga Yuni na shekarar 2010. © REUTERS
Talla

Kotun tace dole Sheikh Al-Maktoum ya biya Gimbiya Haya Bint Al Hussein wadda take kanwar Sarki Abdallah na Jordan Fam miliyan 251 da rabi nan take, da kuma bada wata kadarar banki na Fam miliyan 290 domin kula da ‘yayan su guda biyu tare da jami’an tsaron da suke kare lafiyar su.

Gimbiya Haya ta maka Sheikh Al Maktoum mai shekaru 72 dake shugabancin Dubai a gaban kotu ne inda ta bukaci raba auran su da kuma biyan ta kudade.

Gimbiya Haya Bint al-Hussein kanwa ce ga Sarki Abdallah na Jordan
Gimbiya Haya Bint al-Hussein kanwa ce ga Sarki Abdallah na Jordan Adrian DENNIS AFP

Mai shari’a Philip Moor yace umurnin biyan wadannan makudan kudade ya biyo bayan bukatar kula da tsaron matar da kuma kare lafiyar ta, tare da na ‘yayan ta wadanda ake fargabar cewar mahaifin su wanda shine mataimakin shugaban kasar Daular Larabawa kuma Firaminista na iya amfani da karfin mulki wajen kwashe su.

Alkali Moor yace iyalan Haya na bukatar tsaro sosai, saboda barazanar da suke fuskanta daga mahaifin su.

Kotun ta kuma samu Sheikh Al Maktoum da laifin bada umurnin amfani da na’urar dake sauraron wayar tsohuwar matar ta sa da kuma mayar da wasu ‘yayan sa guda biyu zuwa Dubai ba’a san ran su ba.

Gimbiya Haya bint Hussein
Gimbiya Haya bint Hussein AFP/File

Mai shari’a Moor yace ya bada umurnin biyan wadannan makudan kudade a matsayin kudin sallama ne saboda dukiyar da ya mallaka da kuma irin rayuwar kasaita da iyalan sa suka saba.

Sheikh Al Maktoum wanda bai halarci zaman kotun ba yace yana biyan Fam miliyan 18 a matsayin kudin kula da yaran sa kowacce shekara, tare da Fam miliyan 83 na bukatun gidan da suke, da kuma Fam miliyan 9 a matsayin kudin kashewar tsohuwar matar.

Basaraken ya daina biyan wadannan kudade ne lokacin da matar ta gudu daga Dubai zuwa London tare da yaran ta guda biyu, abinda ya tilasta mata sayar da gwala gwalan ta da jakankunan hannu da dawaki akan kudi Fam miliyan 15 domin kula da ‘yayan ta.

Gimbiya Haya da angonta Sheikh Mohammed bin Rashed al-Maktoum  da wan ta Sarki Abudllah II na Jordan
Gimbiya Haya da angonta Sheikh Mohammed bin Rashed al-Maktoum da wan ta Sarki Abudllah II na Jordan ROYAL PALACE/AFP/File

Tsohuwar matar ta gabatarwa kotu da takardun kudaden da ta kashe da suka kai sama da Fam miliyan 14 a shekara da suka hada da sayen motocin hawa guda 5 akan Fam dubu 130 kowanne guda.

Hukuncin kotun ya kuma kunshi rahotan biyan sama da Fam miliyan 6 da rabi ga masu tsaron lafiyar ta guda 4 wadanda suka zarge ta da lalata da daya daga cikin su.

Sheikh Al Maktoum ya bayyana haka a matsayin shaidar da aka gabatarwa kotun na cewa ta kashe kudaden da aka ware domin kula da lafiyar ‘yayan ta guda biyu.

Yayin da lauyoyin tsohon mijin suka tambaye ta dalilin sayawa yaron ta guda motoci guda 3, sai ta ce tayi haka ne saboda ya saba da rayuwar kasaita.

Yadda Al Maktoum ya sauya fasalin Dubai
Yadda Al Maktoum ya sauya fasalin Dubai AFP PHOTO / Mohamed Samaaha/ EGYPTIAN PRESIDENCY

Gimbiya Haya tayi karatu a Jami’ar Oxford kuma ta wakilci Birtaniya a gasar Olympics da akayi a Sydney a shekara ta 2000, kafin auran Sheikh Mohammed a matsayin matar sa ta biyu a shekarar 2004.

Kotun tace Al Maktoum ya saki Gimbiya Haya ce a karkashin dokar Islama ba tare da sanin ta ba.

Yanzu haka ita da ‘yaran ta guda biyu masu shekaru 13 da 9 suna zama a wani gida kusa da Fadar Kensington da kuma wani gida a rukunin gidajen dake Yammacin birnin London da ta gada daga mahaifin ta Sarki Hussein na Jordan.

Sheikh Al Maktoum na da alaka sosai da Sarauniya Elizabeth ta Biyu, inda dukkan su ke shawa’ar sukuwar dawaki, yayin da iyalan gidan sa suka mallaki garken dawaki a Birtaniya da wasu kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.