Isa ga babban shafi

Putin da Xi sun jaddadawa juna goyon baya don kalubalantar yammacin duniya

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wata ganawa da takwaransa na China Xi Jinpin yau alhamis, karon farko da shugabannin biyu aminan juna ke ganawa fuska-da-fuska tun bayan faro yakin Moscow a Ukraine, inda dukkaninsu suka jaddada ci gaba da baiwa juna cikakken goyon baya don kasancewa masu karfin fada aji a Duniya.

Ganawar shugaba Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping.
Ganawar shugaba Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping. AP - Egor Aleyev
Talla

Yayin taron hadin kan kasashen gabashin Asiya na SCO da ke gudana a Uzbekistan, guda cikin kasashen tsohuwar tarayyar Soviet, shugaba Putin da Xi sun jaddada aniyar ci gaba da kalubalantar kasashen yammacin Duniya tare da bijirewa tsare-tsarensu.

Shugaban Xi Jinpin da Vladimir Putin sun zauna a kusa juna yayin ganawar ta su wadda kowannensu dogarinsa ke kusa da shi, inda bayanai suka ce sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawar yau alhamis a gefen taron na SCO da ke gudana tsakanin yau da gobe, inda suka tabo batutuwa masu alaka da yakin Rasha a Ukraine da kuma barazanar tsaro a yankin.

Halartar taron na Uzbekistan shi ne balaguro na farko da shugaba Xi ke yi zuwa wata kasa tun bayan bullar cutar corona haka zalika taron ya kasance wani salon kalubalantar kasashen Duniya tare da nuna cewa yankin bazai goyi bayan kudirin mayar da Putin saniyar ware.

Yayin ganawar shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa China za ta hada hannu da Rasha don kasancewa a sahun masu karfin fada aji tare da taka rawar samar da zaman lafiya da kuma kawar da rudanin da duniya ta tsinci kanta a ciki.

A bangare guda Putin wanda ke nuna cikakken goyon baya ga matakin China kan yankin Taiwan ya ce yunkurin wasu kasashe na mayar da saura ‘yan amshin shata bazai samu karbuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.