Isa ga babban shafi

Kasashen Larabawa sun shirya taron gaggawa kan rikicin Sudan da Syria

An ta jiyo amon harbe-harbe da fashewar bama-bamai a birnin Khartoum a rana ta 20 a jere, lamarin da ya bar yunkurin tsagaita bude wuta na baya-bayan nan cikin , kwana guda bayan da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya amince da cewa kasashen duniya sun gaza shawo kan rikicin Sudan.

Wani taron kungiyar kasashen Larabawa d aka gudanar a Tunisia karo na 30 a shekarar 2019
Wani taron kungiyar kasashen Larabawa d aka gudanar a Tunisia karo na 30 a shekarar 2019 © AFP
Talla

A birnin Khartoum, shaidun gani da ido sun bayar da rahoton amon fashewar wani abu da kuma musayar wuta a kan tituna da sanyin safiya.

Yanzu haka ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa sun shirya gudanar da wani taro a ranar Lahadi domin tattaunawa kan rikicin Sudan da kuma Syria, gabanin taron kolin da za a yi a Saudiyya a karshen wannan wata, kamar yadda wani jami’in diflomasiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Kusan fararen hula 450,000 ne suka tsere daga gidajensu tun lokacin da aka fara fadan, in ji Hukumar Kula da ‘yan gudun hjira ta Duniya, ciki har da fiye da 115,000 da suka nemi mafaka a kasashe makwabta.

Tun bayan hambarar da Omar El-ashir a juyin mulkin shekarar 2019, masu shiga tsakani na kasa da kasa suka yi ta kokarin kawo fararen hula da sojoji kan teburin tattaunawa.

Sai dai masu sharhi sun yi imanin cewa, Al- Burhan da Daglo sun taka rawa sosai, a juyin mulkin da ya kawo cikas ga mika mulki ga farar hula, kafin su fara aukawa juna saboda neman mulkin kasar da ke Arewa maso Gabashin Afirka.

Yakin da aka kwashe shekaru 12 ana gwabzawa a Syria ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 500,000 kuma kusan rabin al'ummar kasar yanzu na gudun hijira ne ko kuma sun rasa matsugunansu.

Har yanzu dai ba a san adadin yankunan da basa hannun gwamnati ba, amma Shugaban na Syria, Bashar al-Assad na fatan daidaita dangantakar da ke tsakaninsa da kasashen yankin Gulf domin taimaka masa sake gina kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.