Isa ga babban shafi

Masana tarihi sun soki fim din da Netflix ya haska kan tarihin sarauniya Cleopatra

Wani fitaccen mai binciken kayayyakin tarihi na Masar ya fitar da wani shirin fim kan tarihin rayuwar Cleopatra, a dai dai lokacin da shi ma dandalin kallon fina-finai na Netflix, ya fara yada na sa shirin fim din kan tarihin gawurtacciyar Sarauniyar, wadda ya nuna a matsayin bakar fata, lamarin da ya janyo cece-kuce.

Wani dadadden zanen Sarauniya Cleopatra da ta yi zamani shekaru 30 kafin haihuwar annabi Isa.
Wani dadadden zanen Sarauniya Cleopatra da ta yi zamani shekaru 30 kafin haihuwar annabi Isa. Fondation Casa di Risparmio, Fano
Talla

Masana da wasu jami’ai masu ruwa da tsaki kan tarihi a kasar Masar sun shafe makwanni suna caccakar shirin fim din na dandalin Netflix, wanda a cikinsa ya nuna jarumar fina-finai yar Birtaniya Adele James a matsayin Sarauniya Cleopatra, matakin da masanan suka yi watsi da shi suna masu nanata cewar ainahin Sarauniyar farar fata gare ta sabanin mai duhun da aka nuna, a karkashin shirin da Jada Pincket Uwargidan tauraron fina-finan masana’antar Hollywood Will Smith ta jagoranta.

Wannan dambarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da shi kuma masanin binciken kayayyakin tarihi, kuma tsohon minista a fannin, wato Zahi Hawass, ya wallafa na sa shirin fim din ta  kafar Youtube mai tsawon mintuna 90, da ya yi wa lakabi da "Cleopatra"shirin da ya ce ya na kunshe da sahihin tarihin gawurtacciyar Sarauniyar Daular karshe ta Ptolemaic da cibiyarta ke Masar shekaru aru aru da suka gabata.

Cleopatra dai ita ce Sarauniya ta karshe da ta jagoranci kakkarfar daular Ptolemaic, masarautar da ta samo asali daga Girka, daular da kuma tarihi ya nuna cewa ta mulki kasar Masar a tsakanin shekara ta 332 zuwa shekara ta 30 kafin haihuwar Annabi Isa.

Binciken masana ya tabbatar da cewar, Sarauniyar da aka haifa a kusan shekara ta 69 kafin haihuwar Annabi Isa kyakkyawar gaske ce, sai dai shekaru da dama bayan shudewarta aka gaza samun tabbas akan tsarin shiga da kuma launin fatarta, lamarin da ya janyo zazzafar muhawara.

Ya zuwa karshen watan Afrilun da ya gabata dai, sama da mutane dubu 40 suka rattaba hannu akan tuhumar dandalin fina-finan Netflix, da yunkurin sauya tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.