Shugaban Wagner na cikin Rasha - Lukashenko
Shugaban kasar Belarusse Alexandre Loukachenko a ranar alhamis 6 ga watan Yili 2023 ya tabbatar cewa, har yanzu shugaban gungun dakarun hayar kamfanin Wagner, Evguéni Prigojine, na cikin kasar Rasha, duk da yarjejeniyar da aka cimma ta komawarsa a Biélorussie bayan tawayen da ya yi wanda bai cimma nasara ba na ranar 24 ga watan yunin da ya gabata. Kamar yanna . sabanin tabbacin da Alexandre Loukachenko ya bayar a ranar 27 ga watan yuni cewa Evguéni Prigojine na kasar Belarusse.
Wallafawa ranar:
A game da abinda ya shafi Prigojine, yanzu haka yana a Saint-Pétersbourg. Baya cikin kasar Belarusse, kamar yadda shugaba Loukachenko ya sanar wa wani taron manema labarai a alhamis din nan 6 ga watan Yuili.
A cewarsa, a halin yanzu su ma mayakan Wagner, na ci gaba da kasancewa a sansanoninsu, ba a kasar Belarusse ba.
A nata bangaren fadar shugabancin kasar Rasha Kremlin, ta tabbatar da cewa ba ta zura ido a kan shugaban na Wagner. Kakakin fadar Kremlin, Dmitri Peskov, ne ya sanar da manema labarai cewa, ba sa zura ido a kan kai da kawon da shugaban na Wagner ke yi a halin yanzu. Tare karin cewa, a wani sa’in, shugaban Rasha Vladimir Poutine na tattaunawa sosai da takwaransa na Belarusse Alexandre Loukachenko kan zancen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu