Rasha ta fara girke makaman nukiliya masu cin gajeren zango a Belarus
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ya ce kasarsa ta fara karbar kananan makaman nukiliyar Rasha masu cin gajeren zango, wadanda ya ce karfin wasunsu ya ninka na nau’in bam din atomic da Amurka ta taba amfani da shi a kan Japan har sau uku.
Wallafawa ranar:
Matakin dai shi ne irinsa na farko da Rasha ta dauka tun bayan rugujewar Tarayyar Soviet.
A ranar Juma’ar da ta gabata shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar kasarsa, za ta ci gaba da sanya ido kan makaman nukiliyar da za ta fara jibge su a kasar Belarus, bayan shirya musu wuraren ajiya na musamman.
A watan Maris na kuma shugaban na Rasha ya bayyana cimma yarjejeniyar girke makaman a Belarus, inda ya alakanta daukar matakin da yadda Amurka ke tura n ata makaman nukiliyar masu cin gajeren zango, zuwa kasashen Turai cikin shekaru da dama da suka gabata.
Tuni dai Amurka ta caccaki matakin na Putin, duk da cewa ta bayar da tabbbacin cewa ba ta da aniyar sauya matsayinta kan manyan makaman nukiliya, kuma ba ta ga wasu alamun da ke nuna cewa Rasha na shirin yin amfani da na ta ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu