Isa ga babban shafi

Kungiyar BRICS ta karbi sabbin mambobi 6

Shugabannin kasashen BRICS, wato Kungiyar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa sun gayyaci Saudiyya da Iran da Masar da Argentina da Hadaddiyar Daular Larabawa da su shiga cikinsu, a wani matakin fadada kungiyar da burinta shi ne yin gogayya a fannin tattallin arziki da takwarorinta na kasashen yamma.

Baki ya zo daya a game  da karbar karin manbobi a taron BRICS.
Baki ya zo daya a game da karbar karin manbobi a taron BRICS. © brics2023.gov.za
Talla

Wannan fadada kungiyar da jagororinta suka yarje wa, zai bude hanya ga sauran gwamman kasashe da suka nuna sha’awar shiga kungiyar da ta kunshi  Brazil da Rasha da India da China da Afrika ta Kudu a daidai lokacin da rarrabuwa ta fannin bangaranci ke ingiza China da Rasha wajen habaka kungiyar, ta inda za ta iya gogayya da kasashen yammacin Turai.

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda yake karbar bakuncin wannan taro ya sanar a yau  Alhamis cewa, a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2024 ce za a karbi wadannan sabbin  kasashe a hukumance.

Shugabannin kasashen Kungiyar BRICS a birnin Johannesburg
Shugabannin kasashen Kungiyar BRICS a birnin Johannesburg AP - Alet Pretorius

Muhawara a kan karin mambobi a kungiyar ce ta mamaye tattaunawar da aka yi a taron na Afrika ta Kudu, wanda ke gudana a birnin Johannesburg kuma a yayin da dukkannin mambobi suka bada goyon baya ga batun fadada kungiyar, an samu rarrabuwar kawuna a kan yawan wadanda za a kara da kuma lokacin da za a karbe su.

Sama da kasashe 40 ne suka bayyana aniyar shiga wannan kungiyar ta BRICS, a cewar jami’an Afrika ta Kudu, kuma 22 sun mika bukatar hakan a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.