Isa ga babban shafi

An bude taron yanayi na COP28 a birnin Dubai na Daular Larabawa

Akalla wakilan kasashe kusan 200 ne su ka hallara a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa don halartar babban taron yanayi na COP28, a wani yanayi da kasar, wadda mamba ce a kungiyar OPEC ke kokarin jagorantar shirin yaki da amfani da sinadarai masu gurbata yanayi ba tare da kaurace wa amfani da makamashin fetur da gas ba.

Taron dai zai fayyace makoma kan matsin lambar da kasashe masu arzikin man fetur ke fuskanta kan rage gurbata muhalli.
Taron dai zai fayyace makoma kan matsin lambar da kasashe masu arzikin man fetur ke fuskanta kan rage gurbata muhalli. REUTERS - AMR ALFIKY
Talla

Wannan yunkuri na hadaddiyar daular larabawa tuni ya samu karbuwa daga kasashe masu arzikin man fetur kuma ana ganin zai iya haddasa rarrabuwar kai tsakanin masu fafutukar yaki da dumamar yanayi game da hanyoyi da za a bi wajen kai wa ga nasarar yakar matsalar.

Wasu daga cikin kasashe sun yi amannar cewa ta hanyar daina amfani da makamashin Coal, man fetur da kuma gas ne kadai za a iya magance matsalar ta dumamar yanayin tare da maye gurbinsu da fasahar amfani da hasken rana ko iska da sauransu.

Jagoran taron na Cop28 Sultan al-Jaber kuma shugaban kamfanin makamashi na hadaddiyar Daular Larabawa.
Jagoran taron na Cop28 Sultan al-Jaber kuma shugaban kamfanin makamashi na hadaddiyar Daular Larabawa. AP - Kamran Jebreili

Taron wanda aka faro yau Alhamis 30 ga watan Nuwamba za a kai har zuwa 12 ga watan Disamba ana gudanar da shi gabanin karkarewa, kuma a wannan karon taron na shekara-shekara na zuwa ne a wani yanayi da alkaluman ke nuna cewa shekarar bana ta 2023 ita ke matsayin mafi tsananin zafi wadda ke da nasaba da sauyin yanayi.

Gabanin wannan taro dai hukumar kula da makamashi ta Duniya IEA ta fitar da sanarwar da ke bayyana matsayarta na kalubalantar yunkurin na Dubai, ta na mai gargadin cewa wajibi ne kasashe su nemi fasahohin da za su maye musu gurbin makamashi masu gurbata muahallai.

Wannan sanarwa ta IEA ta nanata tare da kalubalantar rawar da makamashin fetur gas da kuma coal ke takawa wajen gurbata muhalli.

Yanzu dai hankula sun karkata ga Sultan al-Jaber shugaban kamfanin makamashi na hadaddiyar daular larabawa da zai jagoranci taron na COP don ganin ko zai sabawa yarjejeniyar yaki da matsalar ta dumamar yanayi ko akasin haka.

Akwai dai fargabar tattaunawar kasuwanci ta mamaye taron fiye da tattaunawa kan yanayi kamar yadda wasu masana suka yi hasashe ganin cewa akwai kamfanoni da daidaikun ‘yan kasuwa baya ga masu fafutuka dama wadanda aka gayyata fiye da mutum dubu 70 da suka yi rijistar halartar taron, adadi mafi yawa fiye da kowanne taron yanayi da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta.

Manyan kusoshin da za su halarci taron sun hada da Firaministan India Narendra Modi da Sarki Charles na Ingila ko da ya ke Joe Biden zai kauracewa taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.