Isa ga babban shafi
COP 28 - SAUYIN YANAYI

OXFAM tayi gargadin cewar asusun sauyin yanayi zai jefa wasu kasashe cikin bashi

Afirka – Kungiyar Oxfam tace ta gano cewar sama da rabin kudaden da manyan kasashen duniya zasu zuba cikin asusun na musamman domin tallafawa kasashen dake shan radadin sauyin yanayi, na iya dada jefa su cikin tsananin bashi, maimakon taimaka musu.

Fati Nzi-hassan, Daraktar Oxfam a Afirka
Fati Nzi-hassan, Daraktar Oxfam a Afirka © rfi Hausa
Talla

Wata sanarwar da kungiyar ta fitar yau, wanda ya nemi sake fasalin biyan kudaden da aka ware domin taimakawa kasashen dake fama da tashe tashen hankula tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020, Oxfam ta gabatar da banbancin kudaden da mutanen dake wadannan kasashe zasu samu, wanda aka kimanta cewar kowanne mutum guda zai samu akalla sama da dala 13 da rabi kowacce shekara.

Kungiyar tace wadannan alkaluma sun gaza dala 6 da centi 68 da aka tsara bai wa mutanen da ake fama da tashin hankali a cikin kasashen su, abinda zai basu damar ci gaba da fuskantar illar sauyin yanayin.

Masu hankoron kare muhalli ke zanga zanga a Dubai
Masu hankoron kare muhalli ke zanga zanga a Dubai © AFP / KARIM SAHIB

Oxfam tace akwai wagegen gibi a tsarin raba kudaden, tsakanin kasashen dake zaman lafiya da kuma wadanda ake fama da tashin hankali a cikin su.

Tsarin ya nuna cewar kowanne mutum a Yankin Tuvalu zai samu dala sama da dubu guda kowacce shekara, yayin da mutum guda a Syria zai samu kasa da dala guda kacal.

Kungiyar tace babu tantama irin kudaden da wadannan kasashe dake fama da matsalar sauyin yanayi zasu samu, yayi kadan matuka.

Oxfam ta kuma kara da cewar, binciken da ta gudanar ya nuna sama da rabin kudaden da za’a zuba, za’a mayar da su ne ta hanyar rance da kuma hanyar yafe bashin da zai dada jefa kasashe matalauta cikin karin talauci.

Kungiyar tace a shekarar 2022, kashi 78 ko kuma kasashe 29 aka sanya a matsayin wadanda ke fama da matsakaicin bashi sun samu kashi 10 daga wannan asusu a matsayin bashi, ba tare da bayani a kan kudin ruwan dake tattare da shi ba, da kuma lokacin da zasu biya rancen.

Sultan Ahmed Al Jaber shugaban taron COP 28
Sultan Ahmed Al Jaber shugaban taron COP 28 AFP - KARIM SAHIB

Jami’in tabbatar da adalci na kungiyar Oxfam dake kula da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, Safa Jayoussi ya bayyana cewar bai dace wannan tallafi daga asusun  sauyin yanayi ya zama wani tarkon bashi ba.

Jayoussi yace a daidai lokacin da kasashen da suka fi arziki ke taya junansu murnar samar da asusun sauyin yanayin, abin takaici ne yadda aka mayar da yadda za’a raba kudaden a matsayin bashi, abinda ke iya zama bala’i ga mutanen dake cikin kuncin rayuwa, da yadda suke harkokin su na yau da kullum.

Oxfam tayi hasashen cewar mutanen duniya biliyan 2, ko kuma kashi guda bisa 4 na bil Adama na zama ne a kasashen da bai dace a tilasta musu karbar sabon rance ba, saboda yawan wadanda ke kansu.

Kungiyar tace tilasta musu karbar wani sabon bashi zai dada bada damar zabtare kudaden da ake warewa domin yiwa jama’a aiki, matakin da zai dada haifar da illa ga rayuwarsu ta yau da kullum.

A karshe Oxfam ta bukaci bada karin kudaden da za’a sanya su wajen gudanar da ayyukan jinkai da kuma hadin kai tsakanin masu fafutukar sauyin yanayi da masu ayyukan tabbatar da zaman lafiya.

Jayoussi yace lokaci ya yi da za’a samar da wani sabon tsarin da zai bai wa mutanen dake daga muryarsu daga cikin al’ummomin dake fama da matsalar sauyin yanayi,  ta hanyar tallafa musu da kudade da kuma tabbatar da canji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.