Isa ga babban shafi

Yarima William zai karbi wasu ayyukan Sarki Charles - Kafofin yada labaran Birtaniya

ingila – Sakamakon rashin lafiyar da Sarki Charles na Ingila, rahotanni daga kafofin yada labaran Birtaniya sun bayyana cewar ‘dan sa Yarima William mai shekaru 41 zai karbi ragamar tafiyar da wasu ayyukan mahaifin na sa.

Yarima William da uwargidan sa
Yarima William da uwargidan sa © Yui Mok / AP
Talla

Ana saran Yarima William ya fara bayyana a bainar jama’a gobe laraba inda zai halarci bikin bada kyaututtuka da kuma gidauniyar taimakawa marasa galihu.

Rahotannin sun ce rashin kanin Sarkin Yarima Andrew da ‘dan sa Yarima Harry a cikin harkokin gidan sarautar zasu taikaita ayyukan da gidan zai dinga gudanarwa.

Yarima harry da uwargidan sa Meghan
Yarima harry da uwargidan sa Meghan © Evan Agostini / Evan Agostini / Invision / AP

Shi dai Andrew ya janye daga harkokin da suka shafi fadar sarautar ne  sakamakon rahotan dangantakar sa da Jeffrey Epstein mai cin zarafin mata, yayin da Harry, wanda shine karamin ‘dan sarkin ya fice daga gidan sarautar domin kula da matarsa.

Fadar Buckingham tace yayin da Sarki Charles ke jinyar cutar kansa da aka tabbatar yana dauke da ita, zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukan da suka shafi kasa da kuma gwamnati.

Tuni Firaminista Rishi Sunak da ya saba magana da Sarkin sau daya a kowanne mako ya sanar da cewar zasu ci gaba da tintibar da suka saba yi da Basaraken.

Kafofin yada labaran Birtaniya sun ce Sarkin ya ci gaba da karbar jajayen akwatunan dake dauke da tarin takardun gwamnati kamar yadda ya saba kowacce safiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.