Isa ga babban shafi

Za mu iya katse alaka da Amurka saboda Iran - Iraq

Gwamnatin Iraqi ta ce, harin da Amurka ta kai kan kungiyoyi masu dauke da makamai da Iran ke marawa baya a kasar na tunzura gwamnatin Bagadaza wajen kawo karshen aikin kawancen da Amurka ke yi a kasar.

Firaministan Iraqi, Muhammad Shia al-Sudani daga dama tare da kwamandan sojin Amurka, Manjo Janar Joel J.B, yayin wata ganawa a birnin Bagadaza.
Firaministan Iraqi, Muhammad Shia al-Sudani daga dama tare da kwamandan sojin Amurka, Manjo Janar Joel J.B, yayin wata ganawa a birnin Bagadaza. AFP - HADI MIZBAN
Talla

Rundunar sojin Amurka ta ce wani harin da aka kai a ranar Laraba ya kashe wani kwamandan Kataib Hezbollah, wato kungiyar masu dauke da makamai da Iran ke marawa baya a Iraki da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta zarge ta da kai wa dakarunta hari.

Amurka ta sha kai hare-hare akai-akai, inda ta auna kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran wadanda ta ce su ne ke kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan dakarunta a Iraki da Siriya.

A daren Laraba ne babban kwamandan kungiyar, ya mutu a wani harin da jirgin mara matuki ya kai kan wata mota a gabashin Bagadaza.

Mai magana da yawun rundunar sojin Iraqi, Yahya Rasool, ya ce kawancen da Amurka ke jagoranta ya zama sanadin rashin zaman lafiya tare da yin barazanar shigar da Iraki cikin rigingimun da basu shafe ta ba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce fadar White House, tana kai hare-hare a yankin ne ba don kara rura rikici ba, sai don hana barkewar rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.