Isa ga babban shafi

Mutane biyu sun mutu a arangamar da aka yi a wani wurin ibada na India

An kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a arewacin India yayin arangamar da ta biyo bayan lalata wata makarantar kur'ani da wani masallaci a jiya Alhamis, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.

Firaministan India Narendra Modi a New Delhi
Firaministan India Narendra Modi a New Delhi AP - Dar Yasin
Talla

Rahotanni daga yanki na nuni cewa,rikicin ya kuno kai ne a gundumar Haldwani da ke Uttarakhand bayan lalata wadannan gine-gine guda biyu da hukumomin yankin suka bayyana cewa an gina su ba tare da izini ba.

Wani jami'in yankin Vandana Singh wanda ta gabatar da wannan rahoto,ta kuma shaidawa manema labarai cewa "An umurci 'yan sanda da su bindige masu tayar da kayar baya a wurin.

Wasu daga cikin shugabanin Hindu a India
Wasu daga cikin shugabanin Hindu a India © Côme Bastin/RFI

Ta kara da cewa jami’an ‘yan sanda na daga cikin wadanda suka jikkata, an kai su asibiti, inda ta bayyana cewa an kona motoci da kuma jifan ‘yan sandan.

Hukumomin kasar sun ayyana dokar ta-baci, da rufe makarantu, da katse intanet da kuma hana taruwa.

Wadannan tarzoma dai na faruwa ne a wani yanayi na tashe-tashen hankula na addini tun bayan da Fira Minista Narendra Modi ya hau kan karagar mulki a shekara ta 2014, musamman ta hanyar lalata wuraren ibada na musulmai.

Narendra Modi a wurin ibadar Ram à Ayodhya
Narendra Modi a wurin ibadar Ram à Ayodhya © AP/Rajesh Kumar Singh

A ranar 22 ga watan Janairu, a wani karimcin da ke nuna nasarar manufofinsa na kishin addinin Hindu, shugaban ya kaddamar da wani gidan ibada na Hindu a Ayoddya (Uttar Pradesh, ta Arewa) tare da mayar da masallaci wurin ibadar Hindu.

A lokacin, wannan barnar ta haifar da tarzomar addini mafi muni a kasar tun bayan samun 'yancin kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 2,000.

A karshen watan Janairu, wata kotu ta bai wa mabiya addinin Hindu damar yin addu’a a cikin wani masallaci a Varanasi (tsohon Benares), daya daga cikin wuraren da aka fi samun sabani na addini a kasar.

Har ila yau, a karshen watan Janairu, hukumomi sun lalata wani masallaci mai shekaru 600 a New Delhi, bisa dalilin cewa wannan ginin, masallacin Akhonji, yana "ba bisa ka'ida ba" a cikin gandun daji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.