Isa ga babban shafi

Macron ya fara ziyarar kwanaki 2 a India don inganta alakar tsaro da kasuwanci

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya samu kyakkyawar tarba a ziyarar kwanaki biyu da ya fara yau Alhamis a kasar India, a wani yunkuri na karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu baya ga kulla yerjeniyoyin kasuwancin da zai kai ga cinikin makamai.

Macron na gudanar da ziyara a India.
Macron na gudanar da ziyara a India. © AP / Julien de Rosa
Talla

Emmanuel Macron wanda ya sauka a Jaipur babban birnin yankin Rajasthan zai samu tarba ta musamman daga Firaminista Narendra Modi da zasu yi liyafar cin abincin dare tare a dadaddiyar fadar Maharaj ta karni 19 da ke birnin mai dogon tarihi.

Faransa wadda ke kokarin karfafa alakar da ke tsakaninta da India kasa ta 5 mafi karfin tattalin arziki, fadar Elysee ta ce ziyarar manuniya ce kan karfafuwar alakar diflomasiyya da ta tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

A gobe Juma’a Macron zai kasance babban bako a faretin Sojin bikin ranar Jamhuriyyar India na 75 da zai gudana a birnin New Delhi wanda sojojin za su sanya kaya masu launi daban-daban wadanda ke wakiltar al’adun kasar sai kuma raye-raye da rangajin rakuma suma dai da adon launukan baya ga shawagin jirage kamar yadda kasar ta saba a kowacce ranar 26 ga watan Janairu.

Ma’aikatun harkokin wajen New Delhi da Paris sun ce ziyarar za ta taimaka wajen karfafa alakar diflomasiyya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Duk da banbancin da ke tsakaninsu a abin da ya shafi yakin Ukraine, bayanai sun ce Macron zai yi amfani da damar wajen sayarwa India akalla na’urorin harba makaman nukiliya guda 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.